in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG zai yi hadin gwiwa da gwamnatin birnin Shanghai daga duk fannoni
2018-10-08 20:04:18 cri

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kana darektan kwamitin JKS na birnin Shanghai Li Qiang da shugaban babban rukunin gidan rediyo da telibijin kasar Sin Shen Haixiong sun kaddamar da babban ofishin CMG dake yankin mashigar teku ta kogin Yangtse tare

Yau Litinin 8 ga wata babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin wato China Media Group da gwamnatin birnin Shanghai sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a birnin na Shanghai, lamarin da ya alamanta cewa, babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin ya kara samun ci gaban aikinsa inda ya kara yin tasiri ga kafofin watsa labarai a fadin duniya.

A halin yanzu babban rukunin gidan rediyo da telibijin kasar Sin ya zama kafar watsa labarai mafi girma a duniya, haka kuma yana taka muhimmiyar rawa a aikin rediyo da telibijin na kasar Sin, birnin Shanghai ya kasance babban birnin wanda ke sahun gaba matuka a fannin yin gyare-gyare da bude kofa ga waje da kuma samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire. A watan Yunin bana, sassan biyu wato babban rukunin gidan rediyo da telibijin kasar Sin da birnin Shanghai sun taba shirya bikin nune-nunen fina-finai na kasa da kasa karo na 21 tare cikin nasara, hakan ya aza harsashi mai inganci ga hadin gwiwarsu, bisa yarjejeniyar da suka daddale, babban rukunin gidan rediyo da telibijin kasar Sin zai bude rassansa guda biyu a birnin Shanghai, wato babban ofishinsa dake yankin mashigar teku ta kogin Yangtse wato lardunan Zhejiang da Jiangsu da birnin Shanghai, da kuma babban ofishinsa a birnin Shanghai, ko shakka babu lamarin zai yi babban tasiri ga duk fadin kasar ta Sin.

Mataimakin darektan kwamitin JKS na birnin Shanghai kana magajin garin birnin Ying Yong da shugaban CMG Shen Haixiong sun kaddamar da babban ofishin CMG dake birnin Shanghai tare

Babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin zai yi amfani da albarkatun birnin Shanghai domin gudanar da hadin gwiwa mai zurfi daga duk fannoni da gwamnatin birnin, misali shirya manyan ayyukan al'adu, da samar da hidima ga yankin mashigin teku ta kogin Yangtse wato lardunan Zhejiang da Jiangsu da birnin Shanghai, da samar da shirye-shiryen telibijin masu amfani da fasahar zamani ta 4k, da gudanar da ayyukan dake da alaka da wasannin motsa jiki, da fassara fina-finai da wasan kwaikwayo daga Sinanci zuwa harsunan waje da sauransu, haka kuma za su kara karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin watsa labarai a gida da ketare baki daya, a karshe dai babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin zai cimma burin samun ci gaba mai inganci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China