Li Qiang ya godewa babban rukunin CMG saboda ayyukan da ya dade yana yi na maida hankali gami da watsa labarai game da birnin Shanghai. Li ya ce, za'a yi iyakacin kokarin samar da muhalli da hidimomi masu kyau ga bunkasuwar harkokin CMG a Shanghai, don goya masa baya ta yadda zai zama sabuwar muhimmiyar kafar watsa labarai dake taka rawar gani a fadin duniya.
A nasa bangaren, shugaban CMG Shen Haixiong cewa ya yi, a ranar 26 ga watan Satumbar bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga cikar babban gidan talabijin na kasa wato CCTV shekaru sittin da kafuwa, inda ya jinjinawa CMG saboda nasarorin da ya samu tun kafuwarsa, tare kuma da bayyana fatansa ga ayyukansa a nan gaba. A halin yanzu, CMG na nan na kokarin raya harkokinsa daga dukkanin fannoni, don zama sabuwar muhimmiyar kafar watsa labarai mai karfi dake taka rawar a-zo-a-gani a duk duniya. (Murtala Zhang)