Shugaban CMG ya halarci taron dandalin tattaunawa kan harkokin watsa labarai na Asiya


Yau Talata, shugaban babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, Shen Haixiong, ya halarci wani taron dandalin tattaunawa mai taken "harkokin watsa labarai na Asiya yayin da suke fuskantar sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki" wani bangare na dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na kasashen gabashin duniya karo na hudu a kasar Rasha.
A jawanbinsa yayin taron Shen ya yi kira ga kafofin watsa labaran Asiya da su kara karfafa hadin-gwiwa tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, a wani mataki na fito da muryoyin kasashen Asiya.(Murtala Zhang)