Babban Gidan Rediyo da Talibijin na kasar Sin wato CMG, zai bude samfurin allon talebijin na zamani mai dauke da fasahar 4K a ranar 1 ga watan Oktoba, wato kafar CCTV4K. A lokacin, birane 13 ciki har da Beijing da Shanghai da wasu biranen lardin Guangdong za a iya kallo a karo na farko. Budewar samfurin allon talabijin na zamani mai dauke da fasahar 4K ta bayyana alamar kokarin CMG na neman cimma burin raya karfin jagoranci da watsa labaru da kawo babban tasiri a duniya.
Masana sun yi bayani cewa, samfurin allon talabijin na zamani mai dauke da fasahar 4K ya fi inganci, wanda ya yi kamar kallon sinima, kana muryar da aka fitar ita ma ta yi daidai da muryar da aka fitar a gidan sinima, masu kallo za su iya kallo talabijin a gida kamar suna cikin gidan sinima. (Zainab)