Bisa yarjejeniyar, bangarorin biyu za su aiwatar da hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi musayar labarai, watsa labarai cikin hadin-gwiwa da kuma bayar da rahotanni cikin hadin-gwiwa, da kara hadin-gwiwa wajen bada rahotanni a fannonin al'adu da tattalin arziki gami da wasannin motsa jiki, a wani kokari na karfafa dankon zumunta tsakanin jama'ar Sin da Rasha.
Yarjejeniyar ta ce, CMG da RT za su ci gaba da yin hadin-gwiwa ta fuskar watsa labarai ta sabbin hanyoyin sadarwa, ciki har da manhajar wayar salula, da shafin sada zumunta na Intanet da sauransu.
Tun bayan da aka kafa babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a watan Afrilun bana, ya kaddamar da hadin-gwiwa mai inganci da kafofin watsa labaran kasar Rasha da dama, ciki har da kamfanin dillancin labarai na RT, da babban kamfanin talabijin da rediyo na kasar, da kamfanin buga jaridu na Rasha, da gidan talabijin na RT, da kamfanin dillancin labarai na ITAR-TASS da sauransu.(Murtala Zhang)