in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta shirya wani tsari na tabbatar da zaman lafiyar Somalia
2018-11-05 09:55:00 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia (AMISOM) ya sanar a jiya Lahadi cewa, ya tsara wani jadawali wanda zai taimakawa shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro ga hukumomin tabbatar da tsaron kasar Somaliya.

Hukumar AU ta ce shirin wanzar da zaman lafiyar mai taken (CONOPS) 2018, da zarar kungiyar tarayyar Afrika da wasu manyan jami'an kasashen dake ba da gudummawa wajen tabbatar da tsaron kasar Somalin suka amince da shi, zai kasance wani muhimmin mataki a kokarin da ake na mai do da zaman lafiya da tabbatar da tsarin mulkin demokaradiyya a kasar Somalia.

Francisco Madeira, wakilin musamman na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia (SRCC), ya ce shirin CONOPS, wanda AMISOM za ta aiwatar da shi tsakanin shekarar 2018 zuwa 2021, ya kasance zagayen karshe na shirin wanzar da zaman lafiyar AU kana bayan kammala shi ne kungiyar za ta kwashe dakarunta baki daya daga kasar ta Somalia.

Tawagar wanzar da zaman lafiyar ta AU ta ce, dakarunta masu aikin wanzar da zaman lafiyar suna yin hadin gwiwa ne da jami'an tsaron kasar Somalia domin yin aiki tare don samar da dawwamamman zaman lafiya a kasar ta gabashin Afrika ta hanyar tsara dabarun shugabanci a yankuna da AMISOM din ta yi nasarar karbe ikonsu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China