Rundunar tsaron hadin gwiwa ta Amurka da Afrika wato (AFRICOM), ta ce hare-haren ta sama an kaddamar da su ne bisa hadin gwiwa da jami'an tsaron gwamnatin kasar Somaliya.
Rundunar sojojin ta Amurka ta ce sun kaddamar da hare-haren ta sama ne bayan da suka gano wata makarkashiya da mayakan ke shiryawa na yunkurin kaddamar da hari kan jami'an tsaron hadin gwiwar a lokacin da suke aikin sintiri.
Sojojin Amurka, tare da hadin gwiwar dakarun tsaron gwamnatin Somaliya da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika, suna gudanar da aikin tsaro na hadin gwiwa domin murkushe mayakan al-Shabab a Somaliya, da nufin fatattakar kungiyar mai biyayya ga kungiyar al-Qaida wajen hana ta samun sukunin daukar karin mayaka aiki, da ba su horo, don su samu damar kaddamar da hare-haren ta'adanci a ciki da wajen kasar. (Ahmad Fagam)