in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da MDD sun sha alwashin kara tallafawa shirin aiwatar da zaman lafiya a Sudan ta kudu
2018-10-11 09:22:02 cri
Kungiyar hadin kan Afirka ta AU, da MDD sun jaddada ci gaba da ba da goyon baya ga matakan wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu, karkashin yarjejeniyar da aka sanyawa hannu cikin watan da ya gabata.

Jami'an kungiyoyin biyu dai sun bayyana hakan ne, bayan ziyarar ganawa da masu ruwa da tsaki da suka kai kasar tsakanin ranekun 7 zuwa 9 ga watan nan na Oktoba, inda suka tattauna da wakilan gwamnati, da na mata, da jam'iyyun gama kai da 'yan jarida, game da yarjejeniyar da aka cimma.

Da suke yi wa manema labarai karin haske, game da sakamakon ziyarar tasu a helkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, wakilan AU da na MDDr, sun bayyana kwarin gwiwar da suke da shi, game da tabbatar da cimma nasarar yarjejeniyar.

Wakilan sun ce, yana da matukar muhimmanci a shigar da dukkanin sassan Sudan ta kudu, cikin aikin wanzar da zaman lafiya, musamman ma mata. Sun kuma sha alwashi ci gaba da aiki tare da kungiyar IGAD ta raya kasashen gabashin Afirka, da sauran kungiyoyin kasa da kasa domin cimma nasarar da aka sanya gaba.

Yanzu haka Sudan ta Kudu ta shiga shekara ta 5 tana fama da yakin basasa, tun bayan barkewarsa a karshen shekarar 2013. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China