in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara kanana kusan 270,000 ne ke fuskantar barazanar yunwa a Sudan ta kudu
2018-10-18 19:47:46 cri
A kalla yara kanana 270,000 ne ke fuskantar barazanar karancin abinci mai gina jiki, da rashin abincin ma baki daya a kasar Sudan ta kudu.

Kungiyar ba da agajin jin kai ta "Save the Children" ce ta fidda wannan alkaluma, tana mai cewa akwai yara kanana kimanin 20,000, wadanda mai yiwuwa ne su rasa rayukan su, nan da karshen shekarar bana, sakamakon tsananin yunwa dake addabar kasar.

Kungiyar ta ce kusan rabin daukacin al'ummar kasar Sudan ta kudu na fuskantar tsananin yunwa. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China