Ma Zhaoxu ya yi jawabi a gun taron koli na kasashe masu samun matsakaicin kudin shiga wanda babban taron MDD karo na 73 ya gudanar, yana cewa kasar Sin kasa ce da ta samu matsakaicin kudin shiga, kana kasa ce mai tasowa. Ya ce kasar Sin za ta yi kokari tare da kasashe masu tasowa, duk da yanayin sauyi da ake samu a duniya. Kaza lika Sin na tsayawa tsayin daka kan tabbatar da moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, da ci gaba da yin hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare. (Zainab)