in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maria Espinosa ta kaddamar da kamfe game da yaki da roba mai gurbata muhalli
2018-12-05 09:53:55 cri
Shugabar babban taron MDD ta yanzu Maria Fernanda Espinosa, ta kaddamar da gangamin yaki da yaduwar robobi, ko ledoji da ba a iya sabunta amfani da su, a wani mataki na dakile tasirin su wajen gurbata muhalli.

Espinosa ta shaidawa manema labarai a helkwatar MDD dake birnin New York cewa, gangamin ya kunshi burin ganin an wayar da kan al'ummar duniya wajen rage leda ko robobi masu gurbata muhalli karkashin tsare tsaren ayyukan MDD, sai kuma batun yayata wannan manufa, bisa hadin gwiwa da sauran kawaye da hukumomin MDD.

Da take tsokaci game da alkaluman tasirin roba ga muhalli, Espinosa ta ce ana zubar da kaso 80 bisa dari na robobin da ba a iya sabunta amfani da su cikin teku. Kaza lika an yi kiyasin cewa, nan da shekarar 2050, yawan robobin da za su rika yawo a sassan teku zai haura na kifaye.

Jimi'ar ta ce kasashen Antigua da Barbuda, da Norway da wasu karin kasashe mambobin MDD, da hukumomin majalissar masu nasaba da kare muhalli sun shiga wannan gangami na wayar da kai.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu, firaministan Antigua da Barbuda, ya ce kasarsa ce ta farko a yankin Caribbean, da ta kafa dokar dakatar da amfani da leda ko robobin da ba a iya sabunta amfani da su yau shekaru 2 da suka gaba, kuma kawo yanzu wannan doka na ci gaba da aiki. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China