in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron sauyin yanayi na MDD a sabon zagaye
2018-12-04 13:35:25 cri
An bude taron sauyin yanayi na MDD a sabon zagaye a birnin Katowice dake kasar Poland a ranar 3 ga wata, wanda ya kasance taro mafi muhimmanci bayan da aka daddale yarjejeniyar Paris, kuma yin shawarwari kan ka'idojin aiwatar da yarjejeniyar zai yi tasiri ga yadda ake aiwatar da yarjejeniyar ta Paris, da ma batun tinkarar sauyin yanayi a duniya.

A gun bikin bude taron a wannan rana, babban sakataren MDD António Guterres ya yi nuni da cewa, bisa rahoton bambancin fitar da abubuwa masu gurbata yanayi na shekarar 2018, wanda hukumar kiyaye muhalli ta MDD ta gabatar da ranar 27 ga watan da ya gabata, a halin yanzu alkawarin da kasa da kasa sun yi wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata yanayi bai kai burin da aka tsara na nan da shekarar 2030 bisa yarjejeniyar Paris ba. A ganin Guterres, ana bukatar kasa da kasa su sake yin bincike kan alkawarinsu a cikin yarjejeniyar Paris don cimma burin shekarar 2030.

Tawagar wakilan kasar Sin mai halartar taron ta gudanar da taron manema labaru a wannan rana, inda ta yi bayani game da ka'idoji da matsayin kasar Sin a gun taron. Mataimakin shugaban sashen kula da yanayi na ma'aikatar harkokin yanayi na kasar Sin Lu Xinming ya yi bayanin cewa, Sin tana kula da shawarwari kan ka'idojin aiwatar da yarjejeiyar Paris a fannoni uku, wato tabbatar da gama yin shawarwarin cikin lokaci, da fahimta, da aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, da kuma gudanar da yarjejeniyar a dukkan fannoni cikin adalci, da kuma maida hankali ga muhimman fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China