in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron sauyin yanayi na MDD
2018-12-03 10:39:48 cri

An bude taron sauyin yanayi na MDD na sabon zagaye a birnin Katowice dake kasar Poland a ranar 2 ga wata, inda wakilai daga kasashe kimanin 200 za su tattauna kan ka'idojin aiwatar da yarjejeniyar Paris a makwanni biyu masu zuwa, wannan ne muhimmin buri da ake son cimmawa a gun taron a wannan zagaye.

A yayin taron, za a gudanar da taro na 24 na masu daddale yarjejeniyar tsarin sauyin yanayi, da taro na 14 na masu daddale yarjejeniyar Kyoto, da taron farko na masu daddale yarjejeniyar Paris na mataki na uku da sauransu. Shugaban taron sauyin yanayi a wannan zagaye, kuma mataimakin ministan harkokin yanayi na kasar Poland Michal Kurtyka ya bayyana cewa, a makwanni biyu masu zuwa, ya kamata bangarori daban daban su kara yin kokari da kirkire-kirkire don cimma burin da aka tsara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China