in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da kudurin G20 na yaki da sauyin yanayi
2018-12-03 10:35:21 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da sanarwar da aka fitar bayan kammala taron G20 na bana a ranar Asabar, wadda ta tabbatar da kudurin kungiyar na kara kaimin yaki da sauyin yanayi.

Wata sanarwar da aka fitar jiya, ta ce Antonio Guterres ya zakulo wasu muhimman batutuwa 3 daga cikin sanarwar ta G20.

Sakatare Janar din ya ce, sanarwar ta G20, ta tabbatar da mara baya ga ajandar shekara ta 2030 na samun dauwwamammiyar ci gaba, da manufar MDD ta dunkulewar duniyar ba tare da barin kowa ba, tare da alkawarin amfani da dukkan manufofi wajen cimma ci gaba mai karfi da daidaito mai kuma dorewa.

Haka zalika, ta tabbatar da bukatar kara kaimi ga yaki da sauyin yanayi, inda shugabannin kungiyar suka bayyana cikakken goyon bayansu ga kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris a 2015, da su aiwatar da kudurin da suka tsara domin ba da gudunmawa a kasashensu.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, shugabannin kungiyar na sa ran samun kyakkyawan sakamako dangane da taro karo na 24 na kasashen da suka cimma yarjejeniya kan sauyin yanayi da za a fara yau Litinin, 3 ga wata a birnin Katowice na Poland. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China