Da yake gabatar da nazarin ayyukan agaji a duniya na 2019 yayin wani taron manema labaru a Geneva, Shugaban shirin bada agajin gaggawa na MDD Mark Lowcock, ya ce mutane kusan miliyan 132 ne za su bukaci agajin jin kai a shekarar 2019.
MDD da abokan huldarta na da burin taimakawa mutane masu rauni miliyan 93.6 da abinci da matsuguni da kiwon lafiya da ilimi da ba su kariya da sauran wasu bukatun da suka dace.
Jami'in ya kuma yi bayanin cewa, shiryawa da wuri da samar da kudade kamar inshorar hadari da ajiyar kudi don tunkarar matsalar da ka iya tasowa, za su taimaka wajen cike gibin. (Fa'iza Mustapha)