in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin dake Kenya na kara fadada sarrafa hajoji a cikin kasar, in ji jami'in diflomasiyyar Sin
2018-12-05 11:14:48 cri
Jami'in lura da ayyuka a ofishin diflomasiyyar Sin dake kasar Kenya Li Xuhang, ya ce kamfanonin kasar Sin dake hada hada a kasar Kenya, na kara fadada sarrafa hajoji a cikin kasar, tare da samar da karin guraben ayyukan yi ga 'yan kasar.

Li Xuhang, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Talata a birnin Nairobin kasar Kenya, yayin taron martaba sassan da suka yi fice, wajen ba da gudummawar raya harkokin tattalin arziki, wanda kungiyar bunkasa tattalin arziki da cinikayya ko KCETA ta shirya.

Jami'in ya ce kamfanonin Sin na kara mai da hankali ga gudanar da sarrafa hajoji a Kenya, kasancewar sun aminta da kwazo, da kuma burin cimma nasara da al'ummar kasar ke da shi. Kaza lika sun lura da irin sha'awa da al'ummar kasar ke da ita, wajen cudanyar al'adu da yaruwan kasashe daban daban.

Li ya kara da cewa, kamfanoni mambobin KCETA, sun daga matsayin yawan ma'aikata 'yan kasa da suke dauka daga 42,000 a shekarar 2016, zuwa sama da 50,000 a shekarar bana.

Wani rahoto na babban bankin duniya na shekarar 2016 ya nuna cewa, bisa matsakaicin mataki, kamfanonin Sin dake aiki a Kenya na yin hayar 'yan kasar 360, sama da 147 da wasu sauran kamfanonin kasashen waje dake kasar ke dauka aiki.

A nata bangaren, babbar sakatariya a ma'aikatar masana'antu, cinikayya da hadin gwiwar kasashe ta Kenya Betty Maina, ta ce zakulo ma'aikata masu kwazo, da karrama su, shaida ce dake nuna yadda KCETA ke martaba gudummawar ma'aikata masu taimakawa wajen cimma muradun da aka sanya gaba.

Yayin bikin dai an karrama ma'aikata 55, dake aiki a kamfanonin Sinawa daban daban, bisa shafe tsawon lokaci suna ba da gudummawa yadda ya kamata. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China