A gun taron shawarwari da aka gudanar a wannan rana a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya, Mr. Christopher Chika ya bayyana cewa, "A ganina, kasashen Afirka musamman ma Kenya na bukatar wannan bikin baje kolin. Muna shirin kafa wani gidan nune-nune na kayayyakin Kenya, don nuna kayayyakin da muke son fitarwa zuwa kasar Sin."
Jami'in ya kara da cewa, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai halarci bikin, don kaddamar da gidan nune-nunen kayayyakin kasar Kenya. A sa'i daya kuma, akwai kamfanoni masu zaman kansu kimanin tara da suka yi rajistar halartar bikin. (Lubabatu)