in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin kasa na zamani da kasar Sin ta gina yayi jigilar fasinjoji miliyan 2 a Kenya
2018-11-01 10:00:49 cri
Jirgin kasan Kenya (SGR) yayi nasarar jigilar fasinjoji sama da miliyan 2 tsakanin Nairobi zuwa tashar ruwa ta birnin Mombasa tun daga watan Mayun wannan shekarar, jami'in gudanarwar jirgin kasan ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba.

Li Jianfeng, mataimakin janar manajan gudanarwar jirgin kasan na SGR, na kamfanin Africa Star Railway, ya bayyana cewa, jirgin kasan yayi jigilar fasinjoji da suka hada da na cikin gida har da 'yan kasashen waje cikin yanayi mai inganci da kyautatawa abokan huldarsu.

Jami'in ya bayyana hakan ne ga manyan jami'an tsare tsare na kasar Kenya, da 'yan majalisu, da masana da suka fito daga bangarori daban daban da masana aikin jarida a lokacin wani rangadi a tashar jirgin kasan na SGR dake Nairobi a ranar Talata domin duba yadda ake tafiyar da harkokin jigilar matafiya a jirgin kasan da kuma yadda ake tafiyar da ayyukan dakon kayayyaki.

Li yace, jirgin na SGR yayi nasarar dakon kayayyaki da dauyinsu ya kai ton 2,605,000 tun daga lokacin da aka kaddamar da aikin dakon kayayyaki ta jirgin kasan, domin saukaka cunkoso a tashar ruwan Mombasa.

Jirgin kasan jigilar fasinjan na SGR mai suna Madaraka Express ya kawo sauye sauye a harkokin sufuri da kuma kyautata harkokin ciniki a yankin layin dogon mai tazarar kilomita 480 wanda kamfanin kasar Sin yayi aikin gina shi.

Yan majalisun kasar Kenya sun bayyana kwarin gwiwa game da ayyukan sufurin jirgin kasan wanda ya kunshi na jigilar fasinjoji da na dakon kayayyaki a matsayin wani gagarumin sauyi a kokarin da kasar ke yi na tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar.

Shakeel Shabbir, wani mamba ne a majalisar dokoki a gabashin Kisumu dake yammacin kasar Kenyan, yace jirgin kasan na zamani ya bada gagarumar gudunmowa wajen bunkasa cigaban kasar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China