in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya karyata rahotannin Amurka dake cewa kasar Sin ta danawa Afirka "tarkon cin bashi"
2018-11-01 13:59:06 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi amfani da kakkausar murya wajen karyata zargin da 'yan jaridun Amurka ke yi wa kasar Sin, na cewa "Kenya na cikin tarkon cin bashi da Sin ta dana mata", ya na mai jaddada cewa, kasarsa na da nata jadawalin neman bunkasuwa, kana tana son yin hadin-gwiwa da duk wata kasa da take taimaka mata wajen cimma muradunta.

Shugaba Kenyatta ya yi wannan furuci ne a kwanakin baya, yayin da yake zantawa da dan jarida daga kafar watsa labaran Amurka ta CNN, gabannin bikin kaddamar da layin zirga-zirgar jiragen sama daga Kenya zuwa birnin New York kai tsaye, a ranar 26 ga watan Oktobar bana, sa'an nan CNN ta wallafa zantawar a ranar 29 ga watan Oktoba.

A zantawar tasu, dan jaridan CNN, wato Richard Quest bai tabo batun layin zirga-zirgar jiragen saman da aka kaddamar ba, amma ya maida hankali kan batun cin bashi na kasar Kenya, inda sau da dama ya ambata cewa Kenya na cin basussuka daga kasar Sin. Game da wannan batu ne shugaba Kenyatta ya jaddada cewa, ba wajen kasar Sin kadai Kenya ke neman cin bashi ba, har ma da ita kanta Amurka, haka kuma Kenya na neman cin bashi ta hanyar da ta dace ba tare da wata matsala ba. Tun da dadewa, akwai wasu kasashen yammacin duniya gami da kafofin watsa labaransu wadanda suka dinga ruwaito rahotannin karya dake cewa wai "kasar Sin ta dana tarkon cin bashi". Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya taba bayyana cewa, kasar Sin ta bayar da rancen kudi ne ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba. Ya ce Sin na mutunta niyyar gwamnatocin kasashen da suka samu taimako daga wajenta, da zuba kudaden tallafi cikin bangaren inganta muhimman ababen more rayuwar al'umma da dai makamantansu, da taimakawa kasashe mabukata haye wahalhalun bunkasuwa, da inganta kwarewarsu wajen neman ci gaba, ta yadda tattalin arziki gami da zaman rayuwar al'ummar wadannan kasashe za su samu ci gaba mai dorewa, al'amarin da ya samu babban yabo daga gwamnatocin kasashe daban-daban gami da jama'arsu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China