in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta turo wani ayarinta zuwa Beijing domin halartar taron yaki da shan kayan kara kuzari
2018-10-26 11:06:50 cri

Jami'an kasar Kenya, sun iso birnin Beijing na kasar Sin, domin halartar taron karawa juna sani na hukumar yaki da shan kayan kara kuzari ta duniya WADA, wanda zai gudana a wannan makon.

Jami'an sun yi amana cewa, taron zai samar da gagarumin sauyi ga dabarun yaki da laifukan da ake aikatawa tsakanin 'yan wasanni.

Agnes Mandu, Daraktar ilimantarwa da bincike ta hukumar yaki da kayan kara kuzari ta Kenya wato (ADAK), ta ce wayar da kai da horar da matasa za su zamo ginshikan da kasarta za ta yi amfani da su na tabbatar da dorewar yaki da laifukan.

Agnes Mandu tare da Martin Yauma, babban jami'in bincike da ci gaba na hukumar ADAK sun iso babban birnin kasar Sin don halartar taron da hukumar yaki da kayan kara kuzari ta kasar Sin CHINADA, ta karbi bakuncinsa.

Wannan shi ne taron karawa juna sani karo na biyu da hukumar WADA ta shirya, wanda zai gudana har zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

A cewar Martin Yauma, hukumarsu na aiki tare da cibiyar tsara manhajar karatu ta kasar, domin sanya horon yaki da kayan kara kuzari cikin manhajar karatu. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China