in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta kudu ya nada sabon ministan kudi
2018-10-10 11:03:10 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa a jiya Talata ya nada Tito Mboweni a matsayin sabon ministan kudin kasar bayan murabus din tsohon ministan kudin kasar, Nhlanhla Nene.

A matsayinsa na tsohon gwamnan babban bankin kasar Afrika ta kudu, kuma gabanin hakan, shi ne ministan kwadagon kasar Afrika ta kudu, Mboweni yana da cikakkiyar kwarewar aiki a harkokin kudi, tattalin arziki, da tsare tsaren shugabanci, in ji shugaba Ramaphosa.

Ramaphosa ya ce, wanda ya gabaci Mboweni a wannan mukami wato tsohon ministan Nene, ya mika takardar yin murabus daga mukaminsa ne da safiyar ranar Talata, inda ya nemi sauka daga mukamin ministan kudin kasar bayan da aka zarge shi da yin alaka da iyalan attajirin nan Gupta dan asalin kasar Indiya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China