in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya babban taron zuba jari karo na farko na Afirka ta kudu
2018-10-27 16:48:20 cri
An kaddamar da babban taron zuba jari na farko na kasar Afirka ta kudu jiya Juma'a a birnin Johnnesburg, inda shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya gabatar da jawabi a gaban mahalarta taron sama da 1,000 da suka fito daga kasashe daban daban, yana mai fatan masu zuba jari za su sa himma wajen shiga aikin ciyar da tattalin arzikin kasarsa gaba.

An kira babban taron na bana ne karkashin jagorancin gwamnatin kasar ta Afirka ta kudu. A wannan yanayi da ake ciki na rashin tabbas kan tattalin arzikin duniya, Afirka ta kudu ta riga ta samu koma bayan tattalin arziki a cikin watanni 6n da suka gabata, kuma tana fuskantar matsala mai tsanani game da rashin ayyukan yi. Saboda haka, shugaba Ramaphosa ya tsara wani shiri da nufin jawo jarin dala biliyan 100 a cikin shekaru 5 masu zuwa, don inganta farfadowar tattalin arzikin kasar. Babban taron na daya daga cikin muhimman matakan da gwamnatin ta dauka wajen jawo jarin waje.

Da yake jawabi, ban da nuna wa masu zuba jari batutuwan dake jawo hankulansu a fannonin wadatuwar albarkarun halittu, da manyan kayayyakin more rayuwa da kuma amfanin kasar ta Afirka ta kudu wajen jagorantar tattalin arzikin nahiyar Afirka, Shugaba Ramaphosa ya kuma jaddada goyon baya da tabbacin da gwamnatin kasar za ta ba masu zuba jari na kasashen ketare a bangarorin manufofi da dokoki. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China