An bayyana a cikin rahoton cewa, yanzu haka akwai matasa da yara da yawansu ya kai miliyan 3 da suke dauke da kwayoyin cutar kanjamau. Bisa shirin da MDD ta gabatar na neman kau da cutar kanjamau nan da shekarar 2030, an dauki matakai daban daban cikin shekaru 10 da suka wuce, lamarin da ya haifar da ci gaba sosai ga yunkurin kare yara 'yan kasa da shekaru 9 daga cutar kanjamau, sai dai ba a samu ci gaban da ake bukata ba a fannin kare matasa. (Bello Wang)