in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka na bukatar managartan tsare-tsaren inganta masana'antu domin bunkasa kere-keren hajojin fitarwa, in ji wani kwararre
2018-12-05 09:15:36 cri
Wani kwararre a fannin tattalin arziki dake aiki a hukumar raya tatttalin arzikin Afirka ta MDD ko ECA Rodgers Mukwaya, ya ce nahiyar Afirka na bukatar managartan tsare-tsare na inganta masana'antu, domin bunkasa kere-keren hajojin da ake fitarwa zuwa sauran kasuwannin duniya. Mr. Mukwaya ya bayyana hakan ne, yayin taron karawa juna sani game da batutuwan tattalin arzikin nahiyar ta Afirka, wanda ya gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda. Ya ce akwai bukatar daukar wannan muhimmin mataki, duba da yadda kasashen nahiyar ke hankoron fadada kasuwannin su a mataki na kasa da kasa domin inganta cinikayya. Ita ma ana ta tsokacin, jami'a a ofishin shirin samar da ci gaba na MDD Janvier Alofa, ta ce nahiyar Afirka na da karancin managartan tsare tsaren bunkasa masana'antu, wanda hakan ke dakushe ci gaban masana'antun. Ta ce kasashen nahiyar suna bukatar rungumar hanyoyin zamanantar da masana'antun ta, ta yadda za su zamo masu inganci, su kuma iya shiga takarar shiyyoyi, da ta kasa da kasa, a fannin cika muradun samun managarcin ci gaba. (Saminu Hassan)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China