in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda za ta kara zurfafa hadin kai da kasar Sin domin samun moriyar juna
2018-09-20 11:06:14 cri
Ministan kudin Rwanda Uzziel Ndagijimana, ya jadadda kudurin gwamnatin kasar, na kara inganta hadin gwiwa da kasar Sin domin cimma burikansu na bai daya da samun moriyar juna.

Minsitan ya ce Rwanda ta na yabawa goyon bayan da kasar Sin ke bata, yayin da take kokarin cimma muhimman muradunta a bangarorin da suka shafi ababen more rayuwa da aikin gona da kiwon lafiya da horar da ma'aikata.

A nasa bangaren, Jakadan kasar Sin a Rwanda Rao Hongwei cewa ya yi, kasar Sin za ta yi aiki da Rwanda tare da ci gaba da musayar dabarun shugabanci da na samun ci gaba, bisa kiyaye ka'idojin aminci da samun kyawawan sakamako da kauna da fahimtar juna da girmmama darajar abota da tabbatar adalci da kuma kare muradunsu.

Ya ce kasar Sin da Rwanda, za su kara daidaita dabarun samun ci gaba, domin samun moriya a bangarori daban-daban, ciki har da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da lafiyar al'umma da horar da ma'aikata da cinikayya ta intanet da hakar ma'adinai da kiyaye dokoki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China