in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsoffin shugabannin Afrika sun bukaci kasashen nahiyar su warware kalubalen da suke fuskanta bisa amfani da hanyoyi na cikin gida
2018-08-03 10:18:20 cri
Tsoffin shugabannin Afrika, sun ce ya kamata shugabanni a nahiyar da masu tsara manufofi, su karfafa tare da rungumar mafitar da ya samo asali daga cikin gida, domin samun dauwammiyar mafita ga kalubalen da nahiyar ke fuskanta.

Tsohon Shugaban kasar Mozambique Joaqium Chissano, ya bayyana yayin taro na 5 na shugabannin Afrika da aka kaddamar jiya Alhamis a birnin Kigalin Rwanda cewa, kamata ya yi nahiyar Afrika ta samo dabaru na cikin gida da za su kai ta ga cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Ya jaddada cewa, al'ummar nahiyar ne ya fi dacewa su magance kalubalen da suke fuskanta ba tare da wani tasiri daga waje ba, kuma kamata ya yi tun fara yanzu.

Shi ma a nasa bangaren, tsohon shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mahamud, cewa ya yi, ya kamata shugabannin Afrika da masu tsara manufofi, su fara lalubo mafita a cikin gida. Ya kuma bukaci kasashen Afrika su samu kwarin gwiwa da karfin gyara tsarukansu, ta yadda za su dace da al'adun nahiyar.

Taron na yini biyu ya samu mahalarta kusan 100 daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu da malamai da kuma kungiyoyin al'umma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China