in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Rwanda ta fara tantance lafiya masu shiga cikin kasar
2018-08-05 15:31:59 cri
Mahukunta a kasar Rwanda sun fara tantance duk wanda zai shigo cikin kasar, don gudun ko yana dauke da kwayar cutar Ebola, sakamakon sake bullar kwayar cutar a Jamhuriyar demokiradiyar Congo dake makwabtaka ta ita.

Shugaban cibiyar kula da harkokin kiwon lafiya na kasar Malicki Kayumba, shi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yana mai cewa, an dauki wannan mataki ne don tabbatar da cewa, an kawo tare da killace duk wani mai dauke da kwayar cutar.

Ya ce, wajibi ne duk wanda zai shigo cikin kasar, ta iyakar kasar da Jamhuriyar demokiradiyar Congo da Uganda, da filin jiragen saman kasa da kasa dake Kigali da kuma tashoshin jiragen ruwa, a duba lafiyarsa don hana yaduwar kwayar cutar Ebola a kasar.

Kayumba ya ce, duk wanda zafin jikinsa ya kai ma'aunin Celsius digiri 37.5 zuwa sama, an bukace shi da ya je cibiyar lafiya masu kusa don a kara duba lafiyarsa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China