in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawaga ta 19 ta jami'an lafiya masu tallafawa kasar Rwanda sun kama aiki
2018-10-06 16:10:29 cri

Rahotanni daga birnin Kigali fadar mulkin kasar Rwanda, na ce tawaga ta 19, ta jami'an lafiyar kasar Sin masu taimakawa kasar Rwanda, ta karbi aiki daga tawagar da ta gabace ta, yayin wani biki na ban kwana da tsohuwar tawagar da ya gudana a jiya Juma'a.

Da yake tsokaci yayin bikin, babban darakta mai lura da asibitoci, da cibiyoyin kula da lafiyar al'umma a ma'aikatar lafiyar kasar Zuberi Muvunyi, ya ce adadin jami'an lafiya da suka yi aiki cikin tawagogi 18 da kasar Sin ta tura kasar ya kai sama da mutum 200, wanda hakan ke nuni ga irin tasirin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rwanda a fannin kyautata kiwon lafiya.

Muvunyi, wanda ya mikawa mambobin tawaga ta 18, ta jami'an lafiyar Sinawa takardun karramawa, ya ce hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya tsakanin kasashen biyu, ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba a fannoni da dama. Cikin wadannan sassa dai akwai samar da ababen more rayuwa, da raya ilimi, da bude kafofin kara fadada hadin kai ga ci gaban kasar wajen kula da lafiyar al'umma, idan aka yi duba da bukatun 'yan kasar, da burin da ake da shi na hade ci gaban yankin baki daya.

A cewar Xing Yuchun, jami'i a ofishin jakadancin kasar Sin dake Rwanda, tawaga ta 18 ta jami'an lafiyar Sinawa, ta gudanar da ayyukanta ne a asibitin Masaka dake birnin Kigali, da kuma asibitin Kibungo dake lardin gabashin kasar. Ta kuma yi rawar gani wajen kyautata tsarin kula da lafiyar al'umma mazauna yankunan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China