in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagorantar kwamitin Sulhu da kasar Sin ta yi, ya taimaka wajen inganta huldar kasa da kasa
2018-11-30 10:40:51 cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya ce shugabantar kwamitin sulhu da kasar Sin ta yi a watan Nuwamba, ya taimaka wajen nuna goyon baya ga huldar kasa da kasa da ayyukan MDD.

Yayin da kasar Sin ke kammala wa'adinta na shugabancin kwamitin sulhun, Ma Zhaoxu, ya bayyanawa manema labarai cewa, muhawarar karfafa huldar kasa da kasa da rawar da MDD ke takawa, ta samu karbuwa sosai tsakanin kasashe mambobin kwamitin.

Ya kara da cewa, muhawarar da aka yi ranar 9 ga wata, ta ja hankali shugabannin manyan hukumomin MDD, ciki har da Sakatare Janar na majalisar da mai rikon shugabancin zauren majalisar da shugaban hukumar majalisar, mai kula da harkokin tattalin arziki da ma shugaban kotun hukunta manyan laifuffuka ta ICC. Har ila yau kasashe sama da 70 da hukumomin kasa da kasa sun samu wakilci yayin taron.

Ma Zhaoxu, ya ce kasashe masu tasowa da ma wadanda suka riga suka ci gaba, sun dauki hulda tsakanin kasa da kasa a matsayin wajibi. Sun kuma jadadda goyon bayansu ga dokoki da ka'idojin MDD, suna masu kira ga dukkan bangarori da su daukaka tsarin huldar kasa da kasa da karfafa ayyukan MDD da ci gaba da kiyaye dokokin kasa da kasa da kuma hada hannu wajen tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China