Geng Shuang ya nuna cewa, MDD tamkar jagora ce ga hada kan kasashe daban-daban don tafiyar da harkokin duniya. A halin yanzu, kasashen duniya na matukar bukatar MDD mai karfin gaske fiye da kowane lokaci a baya. Kasar Sin za ta ci gaba da girmama ka'idoji gami da manufofin kundin tsarin mulkin MDD, da taimakawa ga daidaita batutuwan da suka jawo hankalin duniya, ta yadda MDD za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa.(Murtala Zhang)