A jawabinsa, Mr. Ma Zhaoxu ya ce, rashin daidaiton ci gaba matsala ce da kasashen duniya ke fuskanta, don haka ya kamata su hada kansu, don tabbatar da ci gabansu.
Ma Zhaoxu ya jaddada cewa, ra'ayin neman ci gaban bangare guda da kariyar ciniki na kawo barazana ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wanda kuma ya jawo damuwa ga kasashen duniya da rashin amincewa a tsakaninsu.
Kullum Sin na adawa da ra'ayin neman ci gaban bangare guda da kuma kariyar ciniki, kuma a ganinta, ya kamata a daidaita sabani da matsaloli yadda ya kamata. Sin na son hada kai da sassa daban daban, don kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci kuma tsakanin bangarori daban daban, don kiyaye muradun kasashen duniya.(Lubabatu)