Yayin ganawar Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan muhimmaiyar rawar da MDD take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da samar da ci gaba, tana kuma goyon bayan tsarin kasancewar bangarori daban-daban da tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa karkashin kulawar MDD.
A nasa bangaren Lajcak ya bayyana godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da take baiwa tsarin kasancewar bangarori daban-daban. Ya ce gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil-Adam da shawarar Ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar za su ba da babbar gudummawa ga kokarin samar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Ibrahim)