in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi maraba da nadin Bachelet a matsayin babbar jami'ar kare hakkin bil-Adam ta MDD
2018-08-13 21:07:32 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa ta yi maraba da nadin Michelle Bachelet a matsayin babbar kwamishiniyar kare hakkin bil-Adam ta MDD, kuma a shirye kasar Sin ta ke ta yi aiki da ita wajen kare hakkokin dan-Adam a duniya.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce babban taron MDD ya amince da nadin tsohuwar shugabar kasar Chile a matsayin sabuwar babbar jami'ar kare hakkin dan Adam ta MDD.

Bachelet za ta maye gurbin jami'in diplomasiyyar kasar Jordan Zeid Ra'ab al-Hussein, inda za ta fara wa'adinta na shekaru hudu daga ranar 1 ga watan Satumban shekarar 2018 zuwa 31 ga watan Agustan shekarar 2022.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China