A yau ne mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya gana da shugaban babban taron MDD karo na 72 Miroslav Lajčák a nan birnin Beijing. A yayin ganawar Wang ya bayyana cewa, kasarsa na fatan tabbatar da neman ci gaba tare da kasashe daban daban bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", za kuma ta ci gaba da goyon bayan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da goyon bayan MDD na ganin ta taka muhimmiyar rawa, kana da ba da taimako wajen kafa tsarin tafiyar da harkokin duniya cikin adalci.
A nasa bangare, Miroslav Lajčák ya bayyana cewa, kasar Sin ce ta ja gaba wajen goyon bayan ra'ayin bangarori da dama, da kokarin shimfida zaman lafiya da ci gaban duniya, MDD na fatan zurfafa hadin kai da Sin a dukkan fannoni. (Bilkisu)