Ya ce sabbin takunkuman hari ne ga daukacin Iraniyawa domin sun shafi al'ummar kasar kai tsaye.
Mohammad Javad Zarif, ya kuma soki Amurkar bisa kakabawa kasarsa takunkumai ba bisa ka'ida ba, yana mai cewa za ta yi nadamar matakin mara hikima da ta dauka.
Ya jadadda cewa, kasar za ta dogara da albarkatunta, kuma za ta rayu har ma ta shawo kan lokacin wuya.
A ranar Litinin ne Amurka ta sanya wasu jerin takunkumai kan bangarorin makamashi da kudin Iran, tare da sana'ar fiton kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)