Yayin ziyarar, Jeremy Hunt zai gana da takwaransa na Iran, Mohammad Javad Zarif da wasu manyan jami'ai.
Tun bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a watan Mayu, Jeremy Hunt ne ministan harkokin wajen yammacin duniya na farko da zai ziyarci Iran.
Makomar yarjejeniyar nukiliyar Iran da matakan kasashen Turai na kare ta, su ne za su zamo kan gaba cikin jerin ajandar ziyarar Hunt.
Zai kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi shiyyar Iran da ma dangantakar Iran da Birtaniya. (Fa'iza Msutapha)