in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta ce Amurka ba ta isa ta hana ta fitar da manta ketare ba
2018-10-29 10:34:08 cri
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Es'haq Jahangiri, ya sanar a jiya Lahadi cewa, Iran ta kammala shirinta na yin watsi da takunkumin da Amurkar ta kakkaba mata inda a ranar 4 ga watan Nuwamba za ta fitar da danyen manta ga kasashen waje.

Gidan talabijin na Press TV ya rawaitao Jahangiri na cewa, gwamnatin Iran ta kammala shirinta na mayar da martani kan batun takunkumin da Amurkar ta yi ikirarin kakkaba mata inda za ta ci gaba da fitar da danyen manta a kasuwannin duniya, inda take sa ran sayar da ganga miliyan guda na danyen mai a kowace rana.

Ya ce burin da Trump bai wuce na azawa kasar takunkumi a bangaren makamashi ba, da nufin takaitawa kasar hanyoyin samun kudaden shigarta a daidai lokacin da kasar ke fama da rikicin tattalin arziki a sanadiyyar yaki.

Jahangiri ya ce, Iran babu abin da ya shafe ta da tasirin ci gaba da sayar da mai nata zai yi wa Amurka, dama tuni Iran ta jima tana sayar da danyen manta sama da ka'idar da aka kayyade mata wanda ta shirya a kasafin kudinta na shekara.

Biyowa bayan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na yin watsi da tattaunawar batun nukiliyar Iran a ranar 8 ga watan Mayu, Amurka ta nanata aniyarta na ci gaba aza takunkumin ga Iran da kasashen dake da alakar kasuwanci da ita wanda a baya aka tsara dagewa Iran din takunkumi karkashin yarjejeniyar mai cike da tarihi wanda Amurkar ta yi fatali da ita.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya wa'adin ranar 4 ga watan Nuwamba ga kasashen duniya dake mu'amalar cinikin mai da Iran da su yanke huldar cinikin. Idan ba haka ba za su fuskanci fushin Amurkar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China