in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Salehi: Kasar Iran tana kara samun nasarori duk da takunkumin da Amurka ta kakabamata
2018-11-12 10:13:42 cri
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salehi, ya ce kasarsa ta samu gagarumin ci gaba duk da takunkumen da kasar Amurka ta kakaba mata cikin shekarun da suka gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito Salehi yana cewa, tun lokacin da kasar Amurka ta kakabawa Iran takunkumi shekaru 40 da suka gabata zuwa wannan lokaci, kasar ta samu nasarori a fannoni daban daban, musamman a fannin tsaro, da makamai masu linzami da bangarori na nukiliya.

Yana mai cewa, sabbin takunkumen da Amurkar ta sanyawa Iran, ba za su hana ta samun ci gaba ba, a cewarsa takunkumen da kasashen yamma ke kakabawa kasar sun zame mata jiki, kuma manufofin Amurka ba sabon abu ba ne ga kasar.

Jami'in ya kuma jadadda cewa, Iraniyawa za su yi kokarin ganin bayan sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa kasarsu, za kuma su ci gaba da baiwa duniya mamaki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China