Da yake jawabi yayin bikin karramawar a fadarsa, Shugaba Macri ya yaba sosai da gagarumin ci gaban da kasar Sin ta samu karkashin shugabancin Xi Jinping da alakar Sin da Argentina da kuma muhimmancin da Sin din ke da shi wajen kiyaye zaman lafiyar duniya da samar da ci gaba na bai daya.
A nasa bangaren, Shugaba Xi ya ce ya ji dadin girmama shi da aka yi bisa karramawar, wadda ya ce alama ce ta 'yancin kan al'ummar kasar da kuma kawancen dake tsakanin al'umar Sinawa da ta Argentina. (Fa'iza Mustapha)