in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Argentina
2018-12-03 10:24:20 cri
A ranar 2 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Argentina Maricio Macri a birnin Buenos Aires na kasar Argentina, inda suka cimma daidaito, da tsara shirin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da bude sabon babi na dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya kamata bangarorin biyu, su ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, da hanyoyin raya su da suka zaba.

Tun daga shekarar bana, an samu matsala kan yanayin tattalin arziki da hada-hadar kudi na kasar Argentina. Kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasar Argentina wajen yin kokarin tabbatar da yanayin hada-hadar kudi na kasar, da yin imani ga makomar bunkasuwar kasar Argentina, da kuma nuna kyakkyawar fata ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Argentina.

A nasa bangare, shugaba Macri ya yi maraba da ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Argentina, da nuna godiya ga kasar Sin, bisa samar da gudummawa da goyon baya ga kasar Argentina, da nuna yabo ga shugaba Xi Jinping, a fannin samar da goyon baya sosai ga taron koli na kungiyar G20 da aka kammala. Ya ce Argentina tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a harkokin bangarori daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China