in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka
2018-12-02 09:54:49 cri

Bisa gayyatar da aka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ci abincin dare tare da shugaban kasar Amurka Donald Trump, jiya Asabar da dare a Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina, inda kuma shugabannin biyu suka gana.

Da aka fara ganawar, shugaba Xi Jinping ya ce, ya yi farin ciki sosai da ganawar. Ya kuma kara da cewa, Sauye-sauye da dama sun faru a duniya tun bayan ganawarsu ta baya. Kuma kasancewar Sin da Amurka manyan kasashe biyu a duniya wadanda ke da muhimmin tasiri, dukkansu na daukar nauyin kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya, don haka, hadin gwiwa da juna shi ne zabi mafi kyau a gare su. Shugaba Xi ya ce ya na son yin amfani da wannan dama, don su yi musayar ra'ayoyi a tsakaninsu, ta yadda za su tsara yadda za a bunkasa huldar kasashensu a mataki na gaba.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China