in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi bayani a kan ganawar da ke tsakanin Xi Jinping da Donald Trump
2018-12-02 11:06:30 cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya bayyana a jiya Asabar cewa, bisa gayyatar da aka yi masa jiyan da dare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ci abincin dare tare da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, a Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina, inda kuma suka gana da juna. Wang Yi ya ce, bangarorin biyu sun shafe tsawon sa'o'i biyu suna musayar ra'ayoyi tsakaninsu, inda suka cimma muhimmin daidaito, wanda zai nuna musu hanyar da za a bi wajen bunkasa huldar kasashen biyu a wani mataki na gaba.

Ministan ya kara da cewa, shugabannin kasasen biyu sun kuma tattauna batun tattalin arziki da cinikayya, inda suka cimma ra'ayi daya na daina kara sanya wa juna kudin haraji.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China