Xi da Trump sun amince cewa, za su dakatar da sanyawa juna sabon harajin kwastam, inda suka bukaci kungiyoyin jami'an tattalin arziki da cinikayyar kasashensu, su gaggauta gudanar da shawarwari, da cimma yarjejeniya tsakaninsu don kokarin cire harajin kwastam da suka kara wa juna.
Kasar Sin tana fatan kara bude kasuwarta da fadada shigar da kayayyaki daga kasashen waje, don daidaita matsalolin cinikayyar dake tsakaninta da Amurka. A ganinta kuma, ya kamata kasashen biyu su himmatu tare, domin maido da dangantakar tattalin arziki da cinikayyarsu bisa turba madaidaiciya, da kuma cimma moriya tare.(Murtala Zhang)