in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun kuduri aniyar daina kara wa juna matakan kayyade ciniki
2018-12-02 11:55:33 cri

Bayan ganawar Shugaban Kasar Sin Xi Jinping da Takwaransa na Amurka Donald Trump, jiya Asabar da dare a birnin Buenos Aires, tawagar wakilan kasar Sin da ke kula da tattalin arziki da cinikayya ta bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito kan batun tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.

Sun ce bangarorin biyu sun kuduri aniyar daina daukar matakan kayyade ciniki a kan juna, ciki har da daina kara kudin haraji da suke sanyawa juna a yanzu.

Har wa yau, kasar Sin za ta kara daukar matakan inganta gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, matakan da za su taimaka ga daidaita wasu matsalolin da ke jan hankalin Amurka. A sa'i daya, Amurka ma za ta yi kokarin daidaita matsalolin da suke jan hankalin kasar Sin.

Shugabannin kasashen biyu sun kuma bukaci tawagogin kasashensu, da su gaggauta yin shawarwari da juna, don soke kudin harajin da suka kara wa juna a wannan shekara, ta yadda za a maido da cinikayyar kasashen biyu kan hanyar da ta kamata.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China