in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje koli kan ci gaban kasashe masu tasowa na shekarar 2018
2018-11-29 11:05:31 cri

Jiya ne, aka bude bikin baje kolin ci gaban kasashe masu tasowa na shekarar 2018 a babbar hedkwatar MDD da ke birnin New York. Bikin da za a shafe kwanaki uku ana yinsa zai nuna irin nasarorin da kasashe masu tasowa ke samu, da ma tattauna yadda za a inganta hadin gwiwa a tsakanin su nan gaba.

A jawabinsa na kaddamar da bikin babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yaba da nasarorin da aka samu bisa hadin kan kasashe masu tasowa. Ya kuma furta cewa, a 'yan shekarun nan da suka gabata, yawan gudummawar da kasashe masu tasowa suka ba kasashen duniya a fannin karuwar tattalin arziki ya zarce kashi 50 cikin dari. Sannan jimillar cinikayya a tsakanin kasashe masu tasowa ta wuce adadin cinikayyar duniya.

A sa'i daya kuma, Mr. Guterres ya bayyana cewa, bikin baje kolin zai yi kokarin ganon sirrin yadda kasashe masu tasowa ke cin gajiyar muradun ci gabansu, domin su amfana da fasahohin da suka samu yayin da suke kokarin neman samun dauwamammen ci gaba.

A nata bangare, Madam María Fernanda Espinosa, shugabar babban taron MDD karo na 73 ta ce, bisa ga yadda kasashe masu tasowa ke bunkasa tattalin arzikinsu, yanzu dangankatar da ke tsakanin kasashen na cikin wani yanayi mafi kyau, tana kuma da cikakken imani ga babban sirrin hadin kan kasashen.

An shirya bikin baje kolin ne a karkashin jagorancin ofishin kula da hadin kan kasashe masu tasowa na MDD, tare da hadin gwiwar hukumomin MDD da abin shafa da ma wasu hukumomi abokan hulda. Bikin ya samu halartar wakilai fiye da 850 daga kasashe mambobin MDD fiye da 120.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China