in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnonin Najeriya sun tattauna game da mafi kankantan albashin ma'aikata
2018-11-15 09:49:54 cri

A jiya Laraba ne gwamnonin jihohin Najeriya 36 suka kira wani taron gaggawa a Abuja, babban birnin kasar, don tattauna batun mafi kankanta albashin ma'aikata.

Taron wanda ake sa ran gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari zai jagoranta, zai yanke shawara ce game kudin da gwamnonin za su iya biyan ma'aikatansu, don kaucewa shiga yajin aikin kungiyar kwadagon kasar.

Shi dai wannan taro yana zuwa ne sa'o'i 48 bayan da kungiyar kwadagon kasar NLC ta yi kira ga shugaba Mohammadu Buhari na Najeriya da ya hanzarta daukar mataki game da sabon tsarin albashin ma'aikatan kasar na Naira 30,000 da aka amince da shi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China