Hukumomin tsaron sun shaidawa manema labarai jiya a birnin Kaduna cewa, an kashe 'yan bindigar ne cikin wasu jerin ayyukan soji da aka fara tun watan Oktoba.
Kakakin ma'aikatar tsaron John Agim, ya ce an kuma kwato bindigogin zamani da alburusai da garken shanu daga bata garin da suka hada da masu sace mutane don neman kudin fansa da masu satar shanu.
John Agim ya kara da cewa, baya ga haka, an ceto mutane 31 da suka hada da yara 18 da manya 13 daga wadanda suka sace su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Haka zalika, ya ce an tsare tsageru 5 da masu kai musu rahoto 2, inda a yanzu suke taimakwa hukumomin tsaro a aikin bincike dake wakana. (Fa'iza Mustapha)