in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da kafa sashen karfafawa mata a gwamnatin Libya
2018-11-01 09:38:24 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Libya UNSMIL, ya yi maraba da kafa sashen tallafi da karfafawa mata da gwamnatin kasar Libya ta yi.

Shirin ya yi kira ga gwamnatin Libya da al'ummomin kasa da kasa su taimakawa gudanar ayyukan sashen.

Shirin ya ce wannan gagarumar nasarar ga matan Libya, karin ci gaba ne ga bukuwan cika shekaru 18 da zartar da kuduri mai lamba 1325 na kwamitin sulhu na MDD kan mata da zaman lafiya da tsaro dake wakana yanzu a fadin duniya.

An kafa Sashen na karfafawa mata ne karkashin sashe na 11 na yarjejeniyar siyasar Libya da aka cimma karkashin MDD, wanda bangarorin adawa suka sanyawa hannu a karshen shekarar 2015 da nufin kawo karshen takaddamar siyasar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China