Wata sanarwa da shirin ya fitar, ta kakkausar suka kan harin na Fug'ha da hukumomi a yankin suka ce aikin ramuwar gayya ne na kungiyar IS.
Harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula 4, inda aka kashe biyu daga cikinsu a bainar jama'a, sannan aka sace a kalla wasu 9.
MDD ta yi kira da a kare fararen hula, sannan dukkan bangarorin dake rikici su tsagaita kai hari kan fararen hula da kadarorinsu, kamar yadda dokokin jin kai na duniya suka tanada
Mutane 5 ne aka kashe da asubahin jiya Litinin a wani hari da aka kai kan wani ginin gwamnati a lardin Jufra dake yankin tsakiyar Libya, wanda ke da tazarar kilomita 650 daga birnin Tripoli. (Fa'iza Mustapha)