in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAMID: An samu ingantar yanayin tsaro a yankin Darfur na Sudan
2018-12-03 09:22:41 cri
Wakilin musamman na hadin gwiwar tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU ko UNAMID a takaice Jeremiah Mamabolo, ya ce ko shakka babu yanayin tsaro ya yi matukar inganta a yankin Darfur na kasar Sudan, duk da cewa akwai sauran kalubale a wasu yankunan.

Mr. Mamabolo ya bayyana hakan ne, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Khartoum, yana mai cewa yanzu haka mutane da dama na komawa gidajen su, sakamakon sauyin da aka samu a yankin na Darfur. To sai dai kuma jami'in ya koka game da tashe-tashen hankali da ake samu a yankin Jebel Marra, tsakanin dakaru masu dauke da makamai da sojojin gwamnati, matakin da ke shafar rayuwar fararen hula mazauna wurin.

Mamabolo ya yi kira ga sassan da ba sa ga maciji da juna, da su komawa teburin shawara domin cimma burin da ake da shi na wanzar da zaman lafiya a Darfur, burin da ya yi daidai da kiraye kirayen da sassan kasa da kasa suka dade suna yi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China